SALAFAWAN GASKIYA
SU WANENE SALAFAWAN GASKIYA? KO KA SAN MU WA'YANDA AKE CEMA SALAFAWA KUWA? To a takaice mu din: Muna daukar akidar mu ne kai tsaye daga littafin Allah da ingantattun hadisan Manzon Allah sallallahu 'alayhi wasallam. Tafarkin mu kuma shi ne tafarkin magabata na kwarai in kaso ka fada da larabci tafarkin Salaf ko kace Salafiyyah. Muna gabatar da fahimtar Sahabban Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam- (wa'yanda sune jagororin Salaf a bayan Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam wa radhiyallahu 'anhum-. Muna gabatar da fahimtar su da maganganun su da maganganun mabiya tafarkin su da kyautatawa na daga jagororin musulunci, na jiya da na yau a kan fahimtocin wa'yanda ba su ba. Muna gane tafarkin mutum dai-dai ne idan ya dace da tafarkin Sahabbai da mabiya tafarkin su da kyautatawa, kuma muna gane tafarkin mutum ba dai-dai bane idan ya saba ma ijma'in magabata din. Muna martani ga dukkan wanda ya saba ma gaskiya na kusa damu ne ko na nesa...