KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA
KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA Allah madaukaki yana cewa: وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ اجْعَلْ هَٰذَا الْبَلَدَ آمِنًا وَاجْنُبْنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعْبُدَ الْأَصْنَامَ [ابراهيم : 35] Kuma ka tuna Ibrahim a lokacin da yake cewa : ya Ubangiji ka sanya wannan gari ya zama amintacce kuma ka nisantar dani da 'ya'ya na daga bautar gumaka (Ibrahim: 35). Annabi Ibrahim -Alaihi al- Salām- yayi addu'a ya roki Allah a kan cewa ya amintar da haramin Makkah kuma sannan ya nisantar da shi da 'ya'yan sa daga bautar gumaka, lallai duk wanda yake neman zaman lafiya da aminci na rayuwar duniya harma da ta lahira to dole ya roki Allah shi kadai, kenan ana rokon ne ga Allah shi kadai, ba'a rokon wanin Allah abin da babu mai iya bayarwa sai Allah, yin haka shirka ne fada ne da Allah din, kuma babu wanda ya isa yayi fada da Allah bare yai nasara, sannan bayan an samu zaman lafiyar kuma to babu abin da zai wanzar da wannan zaman lafiyar ya samu dorewa a samu facakar...